Matar Mutum Page 3




‎sako da sakon nan basa yi da akwai fahinta sosai a tsakaninsu a kuma Bikin Bilkin ya dabbaqa soyayyarsa ga Bara'atu wadda tayiwa Bilki babbar qawa. Tun suna yan yara Audu yake sonta an dauka yarinta ce ashe shi har ransa ya riqe abun yanzun daya furta yana son ta da yawa wasa suka dauki abun saboda idan ka dubi a yanda akewa yara aure Bara'atu ta isa kaiwa daki dukda shekarunta sha biyu ne a sannan amma ga Bilki da take sa'arta an mata aure itama Audu kuwa yana shekara sha bakwai koda Maza suna saurin Aure a qauyen amma be isa ba tukunna, ga Yakubu me sha tara da Aminu me Ashirin da biyu nan basuyi aure ba bare Azo kansa haka dai ya ringa hurewa Bara'atu kunne da soyayyarsa seda ya tabbata ta mato ta yanda ko ya koma birni ba zata saurari wani ba zata jira shi kafin ya koma Birni ya bar Audu da suke hutun makaranta zasu shiga Aji hudu a sannan.

‎Satin Audu daya da tafiya jikin Malam Tijjani ya motsa kuma ciwon yafi na ko yaushe zafi dole Yakubu ya bazamo Kano neman Audu saboda Malam din da yake ta nanata a kira masa Audu gashi babu waya a sannan, kwanansa daya suka juya hankali tashe yanda ya tarar da jikin Mahaifin nasa ya tayar masa da hankali ya shawarci manyan yayyensu akan su tafi da Malam Kano a akaishi Asibiti amma suka qi a cewarsu anayin na gargajiya wai a yanda ya ganshi ma jikin da sauqi, cikin daren Ranar Malam Tijjani ya amsa kiran Ubangiji har yaja numfashinsa na qarshe kuwa be dena maimaita musu su tsaya akan gaskiya ba kuma duk rintai duk wahala karsu yada zumunchi suci gaba da hada kansu kamar yanda suka tashi.

‎Sunyi kuka sosai da jimamin rasuwar mahaifin nasu, daga Audu har Yakubu suka kasa komawa inda suka fito saboda mahaifiyarsu da mutuwar Malam din ta tabata sosai har itama ta kwanta jinya, ita din bata da kowa a yanzu se Malam dasu yayanta dan Iyayenta duk sun rasu Yayyenta biyu suma shekara uku kenan Babban Ya rasu me bi masa kuma be cika shekara da rasuwa ba shima yanzu ga Malam shima ya tafi. Seda sukayi dagaske suka qarfafa mata guiwa kafin ta dangana taci gaba da zaman takaba. Audu ya damu Yakubu akan batun komawa makaranta dan tuni hutu ya qare an Koma amma duk sanda yayi masa maganar se yayi shiru yaqi ce masa komai. Audu be fahimci dalilin Yakubu naqin komawa makaranta ba seda akayi sadakar Arba'in din Mahaifinsu, a ranar kuma dattawan qauyen suka zaunar dasu akan maganar rabon gado.
‎*Batoul Fashion and Boutique* online store ne na sai da kayan 'yan gayu dandasa-dandasa na gani na fada, na kece raini a taro, masu tashin kan Habeeby ❤️ Kuma masu sa kishiya kwalla๐Ÿ˜‚๐Ÿƒ๐Ÿป‍♀

‎*MATAR MUTUM*
‎*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

‎*MARUBUCOYAR*
‎*WATA KISHIYAR*
‎RUBUTACCIYAR QADDARAH*
‎*HALIN KISHI*


‎*FREE PAGE 3*

‎Malam dai sun sani Gona guda daya ya bar musu se gidan da suke ciki, aka raba musu komai yanda shari'a ta tanadar, ba'a samu wani surutu ko hayaniya ba saboda yawansu daya kowanne bangaren sunada Maza uku mata biyu se iyayensu mata. Zancen gida duk sun yarda akan kar a raba iyayensu suci gaba da zama ciki tunda kowa yasan bangaren da yake mallakinsa haka Gona sun yarda akan za'a ci gaba da nomata yanda aka Saba ana raba amfanin kuma lokacin daman yayi daidai dana girbi dan haka kwana kadan akayi girbi aka kawo amfanin Gona gida kuma daman abinda ake dan jalautawar yayi qasa banda ma Audu da ya zo da yan kudade shi yake ta hidima da gidan tun bayan Rasuwar Malam.

‎Su Audu sunyi zaton za'ayi rabo ne matsayin cewar kowa yana da gado cikin abinda aka girbe din amma se sukaga sabanin haka. Sanda akayi rabon baya gida yana gurin Bara'atu yaje tadi. Yakubu da akayi a gabansa kuma kanzil bece musu ba suka kacaccala kayan suka ware musu nasu wanda dama ba dukka aka fito dasu ba kadan aka yafito daga Rumbu aka zuzzuba musu Masara, Gero, dawa buhu bibbiyu Alhalin a shekarar an samu amfanin gona ko wanne launin Abinci yafi Buhu Hamsin amma abinda suka basu kenab se shinkafa da sukeyi wadda yawanci daman ita Siyarwa akeyi to bata isa girbi ba. SedaAudun ya dawo ya tarar da kayan a bakin qofar dakin Dada inda suka ajiye musu, duk da cewar Rumbun gidan a kasonsu ya fado amma su Hashimun sun kulle tulin abinci sun tafi da muqulli. Sanda Malam yana raye duk nan ake ajiye komai duk wadda zatayi girki ta shiga ta diba su kansu su Hashimun sedai su dibi wanda ze ja musu lokaci idan ya qare a kuma diba.

‎Audu ya gama kallon kayan kafin ya shiga dakin Dada suna zaune suna cin tuwon Dawa da Aisha ta tuqa musu suna hira jefi jefi ya ajiye musu qullin soyayyar karfasa daya taho musu dashi Dada ta saka masa Albarka tareda tura masa nasa kwanon tuwon da aka ajiye masa. Kai ya girgiza alamar ya qoshi dan yaci a gidansu Bara'atu, Innarta Da takeyi dashi shiyasa dui sanda yaje gidan seta tisa dole ya shiga in da darene se yaci tuwo tun yana kunya har ya sake dan ko beci ba zata hado shi dashi ya taho gida. Seda ya bari sun gama cin tuwon kafin yayi magana yace
‎"Dada naga Hatsi a qofar daki na waye?"

‎"Yawwa daman kai nake jira ka kamawa Yayanka ku shigar dasu dakin Malam (shima Rabon su ne) wannan uban sakalcin wai baze iya ba" ta nuna Baballiya dake rakube gefen gado wai bacci yake so yayi ita kuma ta hanashi tace se tuwon daya ci ya ratsa masa.
‎"Abinda ban gane ba Dada waya kawo Hatsin?" Ya sake tambayarta. Ta miqe tana cewa
‎"Rabon mune na amfanin gona da aka fitar dasu yayyenku suka raba, to kaga Rumbun nasu ne yanzu shiyasa nace ku saka a dakin Malam tunda nan babu guri"

‎"Wancan abun ne rabon mu rai shida a cikin sama da buhu dari da aka fitar, kenan buhu daddaya muka tsira dashi cikin gadon uban mu ba wai kyaimuta aka bamu ba?" Audu ya fada cikin zafin rai yana miqewa se a sannan Yakubu yayi magana yace
‎"Abinda suka ga ya kamata su bamu kenan kuma kar kace zakayi magana muje mu shigar dakin kamar yanda Dada tace"
‎"Wallahi Baze yuwu ba, banda ma tsabar rainin wayo roqarsu mukayi da zasu tsammana wannan abun ko kuwa? Dole a fito da komai a sake rabo me yasa ma da zasu fara baka kirani ba" yana gama fadar haka fuuu yayi waje Dada da Yakubu na kiransa amma beko saurare su ba yayi dakin Goggo Fadi.

‎Dada da Yakubi sunfi Audu sanin yanayin zaman gidan a yanzu saboda kusan shekara bakwai kenan daya fara zaman birni idan yazo yan kwanaki yakeyi ya koma kuma duk sanda zezo da abin hannunsa dan haka kowa haba haba yake dashi. Yakubu kuwa tunda ya fara makarantar kwana nan yake hutunsa dan haka yasan duk wata kitimurmura dake faruwa tsakanin Goggo Fadi da yayanta da yawan qorafin da sukeyi akan Abinci wanda a cewarsu su suke wahala su Noma Hafsatu da Yayanta sedai kawai suci harda Bilki da ake aikawa dukda shi Mijinta babu laiifi yana da rufin asiri dan haka be shiga cikinsu ana noman tare ba amma in akayi girbi se Malam yasa an loda itama an kai mata acewarsa tana da haqqi cikin gonar.

‎Iyakar qoqari Malam yayi gurin ganin cewar kan Ahalinsa be rabu ba kuma har ya mutu yana musu wannan nasihar wadda kuma sunyi qoqarin boye taciki sun hada kai a gaban idonsa to amma yanzun basa jib zasu cigaba da bautawa Hafsatu da yayanta shiyasa suka fara da haka a ganinsu ma sun musu Adalci da suka basu wannan din ladan Aikin da Malam yayi kafin ya kwanta dama.

‎Audu kuwa da sallama ya shiga dakin Dada yana qoqarin danne bacin ransa, suna zaune ita da Baba da Hashimu suna hira. Ya tsugunna daga gefe ya gaidasu suka amsa fuska a sake kafin sukayi shiru gaba daya. Seda ya saisaita muryarsa ta yanda zasuyi magana cikin risilama kafin yace
‎"Yaya Daman naga hatsi a qofar mune dana tambayi Dada se tace mun wanda aka rana aka fitar mana ne"

‎"Na'am, haka akayi" Hashimu ya fada yana karkacewa dukda cewar shi Audu da Baba yayi magana, shiru suka kumayi ganin da yayi basu da niyyar tanka masa dan Goggo Fadi ma wata hira take neman jefo musu tana tambayarsa yaushe ze koma Birni dan haka yace
‎"Yaya tambaya fa nakeyi shi wancan abun ana nufin shine rabonmu mu biyar da Mahaifiyarmu kenan?"

‎"Ga amsa ka bawa kanka Audu me kuma kake da buqata?" Baban ya magantu sannan yaci gaba da cewa
‎"Ko yayi yawa ne? Tunda kai ba mazauni bane Yakubu ma Makaranta ze koma Innartaku daga ita se Aisha da Baballiya Aisha ma jiya na hadu da Hayatu yake roqar arziqin a basu ita tadan taya Bilki zama inaga an samu qaruwa ne ko yace bata da kafiya dama yanzu nake so idan zan fita na leqa nayiwa Goggon maganar to gaka ma seka shaida mata idan ka koma kaga wannan abinci ai ya isheta ita da Baballiya".

‎Ran Audu ya qara baci amma ya daure murya a daure yace
‎"Amma dai Yaya koda ace cikin Dada ne ita kadai kamata yayi a raba komai kai daya yanda shari'a ta tsara tunda dai muna da gado a ciki wannan ruwan mune bisa Adalci mu qara muku tunda kun fimu buqatar abincin"

‎"Babu shakka rashin kunya zaka manq Audu mu kake kallo kana cewa mun fiku buqatar abinci wato ga mayunwata ko?" Goggo Fadi ta fada tana tafa hannu. Ko a jikinsa yace
‎"Ni ba abinda nake nufi ba kenan Goggo, nufina su Yaya suna da Iyalai mu kuwa bamu da nauyin komai kamar kuma yanda ya fada mu ba mazauna bane dan haka abincin zeyi mana yawa ku kuma ya muku kadan"

‎"To yanzu me kake so ayi?" Baba ya tambayeshi, Audu ya gyara zama yace
‎"Rabo za'a sake na gaskiya a fitarwa da kowa haqqinsa idan ma ta kama a kirawo su Liman da me gari su raba"
‎"To ba za'ayi hakan ba ubanmu, kai karfa kaga wai ka fara riqe yan kudade ka dauka kafi mu ko zamu bika to baka isa ba wlh da zaka zo kana yiwa mutane magana da sigar umarni. Bari ma kaji wannan rabon da kaga an baku dan dai Goggo ta saka baki ne amma da mu bamuyi niyyar baku kamar hakan ba saboda babu guminku ciki mu muka sha wahala muka noma abinci dan haka daga yanzu in har kuna son kuci abinda aka noma cikin gonar nan to sedai ku shiga ayi daku" Hashimu ya fada, Audu ya kalle shi kafin ya miqe yana cewa

‎"Amma dai muna da gado a cikin gonar ko?"
‎"Su kuma ai ba bayin ubanka bane da zasu sha wahala su noma kuna zaune su baku kuci" Goggo Fadi da se yanzun ta saka musu baki ta fada wannan ya tabbatar masa da cewar shawararsu daya dan haka ya fice yana cewa
‎"Ai kuwa in har haka kuka zaba sedai a raba gonar idan yaso se na gani in abinda kuka samu ze isheku ku noma abincin shekarar". Goggo Fadi ta hau tafa hannu tana salallami wai yazo har daki ya qare musu tanadi.

‎Audu kuwa yana fita dakin da suke kwana ya shige zuciyarsa na tafarfasa dan yasan idan ya koma dakin Dada ma fada zatayi masa ta bashi rashin gaskiya amma ya qudure a ransa kome za'ayi sedai ayi tunda ta haka suka zaba to su zuba su gani su waye zasu sha wahala. Kenan ita Goggo Fadi luf luf tayi musu sanda Malam na raye suke zaune lafiya da Dada shine yanzu daga mutuwarsa ko kwana sittin be cika ba fitina zata fara bullowa daga barayinta. Idan taqamarsu su suke noma gona ai su kuma suna da kaso a cikin qasar ya zama tamkar sun basu aro ne suna biyansu shikenan tunda dai basu hango wannan maslahar ba to za'ayita yanda suke so dan idan rigima ce kowa ya sani kaf karkarar bashida mahadi. Tun yana dan mitsitsi fada ne dashi kamar dage babu randa baz fita wasa ba tareda an kawowa Dada ko Baffa qarar ya daki wani ba shiyasa ma ya dena wasa da sa'anninsa ya shiga cikin su Yakubu amma ko su din idan kaga yanda yake a cikinsu seka dauka ya girme su kura ce tayi lafiya kuma tunda aka tabota kowa ze dandani kudarsa.

‎Yana kwance yana saqa da warwarar ta inda ze bullowa al'amarin, yanzu idan ya koma Birni Yakubu ya koma makaranta kenan zaman gidan in ba'ayi wasa ba gagarar Dada zeyi to kuwa baze taba barin haka ta faru ba. Yakubu ya shiga dakin rai a hade yace ya tashi su kwashe kayancan amma ko gezau Audu beyi ba, daya isheshi da magana yace
‎"Ka qyaleni baza'a kwashe ba se gobe tayi an sake Rabo sannan su kwashe nasu daga Rumbu tunda ai ba rabonsu bane ba"

‎"Audu kasan me kake so ka taso kuwa?" Yakubu ya fada yana zama a gefen qafafunsa Audu ya wuntsila ya tashi zaune yace
‎"Na sani, naje na same su sunce tunda bamu noma ba dan haka iyakar abinda zasu bamu kenan kuna daga yanzun ma muddin muna son Abinci sedai mu shiga ayi Noma damu"
‎"To ai gaskiya suka fada, shiyasa nace maka bazan koma makaranta ba na haqura da karatun zan zauna na kula da Dada dasu Aisha kai kuma ka shirya ka koma Birni kaci gaba da Buga bugar ka" Yakubu ya fada cikin sanyinsa, Audu ya galla masa harara tsabar takaici daya rasa me zece masa kawai yayi tsaki ya koma ya kwanta. Haka Yakubu ya gaji da masa maganar ya tashi su kwashe kayan qarshe se Aminu daya shigo gidan ne ya taimaka masa suka kwashe, shima seda ya tambayi Yakubun kayan menene wannan yayi shiru bece masa komai ba.

‎Daya shiga gurin Goggo Fadi lokacin su Hashimu sun tafi gidajensu ya sake tambayarta nan ta wassafa masa qarya da gaskiya akan Audu, Aminu yayi shiru kafin ya kalli Mahaifiyar tasa yace
‎"Amma zancen gaskiya wannan ba Adalci bane Goggo, wannan hatsin da ake magana fa Malam ne ya noma shi a gonar sa mu duk mun tayashi aiki ne a matsayinmu na yayansa, kinga kenan duk wani Magajinsa yana da rabo daidai da kowa a ciki koda kuwa Jinjirine yau aka haife shi. Sannan maganar kuce idan basuyi Noma ba baza'a basu abinci ba bata taso ba saboda yau idan sukace a raba gonar nan kun sani Kason da zamu samu baze isa mu ringa noma abinda ze riqe mu ba, kuma ko cewa sukayi mu ringa haya muna biyansu bamu da abinda zamu basu. Nidai a ganina ayi maslaha koda kuna ganin ba za'a ringa raba daidai ba tunda mun fisu yawan Ahali a ringa fitar musu da abinda ze ishe su har su saida suyi sauran buqatu hakan duk taimakon kaine".

‎Goggo Fadi tayi kasaqe tana kallonsa kafin tace
‎"Babu shakka Aminu wato Hafsatu da Yayanta sun fimu a gurinka kenan ko?"
‎"Ba abinda nake nufi kenan ba Goggo, ni wlh kece ma kike bani mamaki gaba daya kin biyewa Yaya Hashimu yana doraku akan wata hanya ta daban dan Yaya Baba ma babu ruwansa sedai idan yanzu shima ya dauki hudubar tasa, har Malam yaja numfashin qarshe yana mana nasiha da mu hada kanmu kar mu bari baraka ta shiga tsakaninmu me yasa kuka zauna tsayin shekaru lafiya dasu se yanzu daya mutu sanda yafi buqatar mu hada kai mu cigaba da yi masa addu'a sanann ne kuma fitina da rabuwar kai zata bullo?

‎Kowa ya sani Dada bata da matsala kuma kome zakuyi ba zata daga kai ta kalle ku ba amma ai mutum ya kamata yasan daidai ba se an tunatar dashi ba ina amfani cikin danne haqqin wani wannan abun fa magana ake ta dukiyar marayu da wanda ya cinye kudi da kadarori daku da kuke shirin cin kwayoyin hatsi a gurin Allah baku da banbanci Goggo, nidai shawarata tun wuri ku farga karku bari shaidan yayi tasiri a zukatanku. Yanzu an fara rigima akan Gona gobe kuma se ace za'a raba gida shikenan zumunchin da Malam yake ta mana takarar mu riqeshi kinyi sanadin murqusheshi"

‎"Nice ma zan raba muku zumunchin?" Goggo Fadi da jikinta yayi sanyi da maganganun Aminun ta fada, ya miqe yana cewa
‎"Eh mana saboda duk fitinar da su Yaya Hashimu zasu zo da ita idan kika tsawatar musu dole su bari amma idan kika basu goyon baya kinga gaba zasu qarayi" daga nan ya fice ya wuce can dakinsu inda suke kwana dasu Audu.

‎Tun Asuba da suka fita masallaci Audu be dawo ba kaitsaye qofar gidan Liman ya tafi ya jirashi yana zuwa kuwa ya zayyane masa abinda ya faru dan ya rantse baze bar maganar ba, shirye shiryen komawa Birni yakeyi tayaya hankalinsa ze kwanta a can Alhalin an fara irin haka ga Yakubu yana maganar ze haqura da mafarkinsa saboda ya zauna ya kula da mahaifiyarsu shi kuma baze yarda ba shiyasa zeyi iyakar qoqarinsa yaga komai ya daidaita sannan su rankaya su koma Kano dan yayi rantsuwa muddin yana numfashi seya cikawa Yakubu burinsa na zama Alqali.

‎Liman ya gama jin bayaninsa yace yaje ze samu me gari daga nan za'a kira duka yan uwan nasa su zauna haka akayi kafin yamma duk an kai musu sammaci bayan sallar isha'i suka hallara gaban me gari Hashimu se muzurai yakeyi Baba

Karanta Next Chapter Matar Mutum