Matar Mutum Page 2


kana cewa zaka masa dukan mutuwa me kukeyi hakan"

‎Salim ya daga kai ya kalli Alhajin da wani irin duba kamar wani sa'an sa yace
‎"Shi daya wuce ka tsayar dashi kaji ba'asin zage zagen da yakeyi?"
‎"Ban tsayar dashi ba saboda.."
‎"Base ka fada komai ba saboda shi dan so ne basa laifi, nida ya daukarwa abu nayi magana nine mara gaskiya to se a biyani kudin takalmina idan ba haka ba kuma na rantse da Allah sena kwantar da yaro" Salim ya datse Alhajin babu dar bare shakka tsabar mamaki kallonaa kawai Alhajin ya ringayi ya kasa cewa komai. Shi Audu ne yayi lalacewar da Kalan Hanji a cikin yayansa ze ringa mayar masa da magana?

‎"You are very stupid Salim Alhajin kake gayawa wannan maganar saboda baka da hankali?" Ahmad da shigowarsa kenan ya tarar dasu ya fada, Salim ya kada qeyarsa ya juya yana cewa
‎"Ai gaskiya na fada Yah Ahmad da ace ni na daukarwa Faisal din abu da yanzu an hada Family meeting ance mun barawo shi kuwa tunda dan gaban goshi ne kaga ni ya bawa laifin ina masa hayaniyaba gida a biyani abu na kawai a zauna lafiya" daga haka ya barsu tsaye kamar sokaye saboda mamaki.

‎"Kayi haquri Alhaji gaba dayansu se na bata musu zan zauna dasu" Ahmad ya fada cikin girmamawa, Alhaji ya jinjina kai irin na wanda Idea ta qarewa kafin ya juya ya shige Falonsa maganganun daya sha yau suka masa rufdugu a kwakwalwa tabbas makomar gidansa tana cikin garari, idan kuma beyiwa tukfar hanci ba za'a samu gagarumar matsala.
‎Sama ya haye dakinsa ya zauna bakin gado bayan daya rage babbar rigar jikinaa ya qara gudun Ac, tunanin baya ya shigayi, so yake ya gano bakin zare ta inda ya kuskure ko Allah zesa ya samo hanyar gyarawa. Kamar Film ya shiga hasko rayuwarsa tun daga tushe.
‎*MATAR MUTUM*
‎*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

‎*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

‎*LITTAFIN KUDI NE*
‎*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
‎*7061838488*
‎*OPAY DIGITAL SERVICES*
‎*MARYAM FAROUK*
‎OR
‎*0709290797*
‎*ACCESS BANK*
‎*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
‎*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
‎*NAGODE*

‎*FREE PAGE 2*

‎ABDULWAHAB TIJJANI Shine Asalin sunansa, AUDU da mutane da suka sanshi dashi yasa ake daukar cewa ABDULLAHI shine sunansa kamar yanda duk inda kaji Audu a gurin bahaushe tunanin na karkata da cewar Abdullahi ne sedai shi Alhaji Audu ya samu sunan ne ta dalilin wata kakarsu tun suna yara ya tashi da bala'in son kudi, da sallah idan ya samu yan silallarsa na barka da sallah ya ringa yawo dasu kenan a aljihu yana karkadawa suna qara idan ka tambayeshi menene se yace
‎"Kudina ne tara su zanyi se sunyi yawa sosai" shikenan take kiransa da Audu kudi tun befi shekara biyar a duniya ba kuma sunan ya bishi aka manta da Abdulwahab sedai Audun kawai har girmansa kuma wannan dalili ya saka koda Yaransa suka Shiga makaranta Malamai sukayi musu register da ABDULLAHI TIJJANI BECHI a cewarsu Audu ba suna bane.

‎Alhaji Audu haifaffen wani qauyene da ake kira Bechi cikin qaramar hukumar Kumbotson Jahar Kano. A yanda labari ya iske su kakansu daya haifi Mahaifinsu Tijjani wato Malam Lawan shine me garin Bechi na farko ance seda suka shekara Talatin da matarsa Asabe kafin Allah ya basu haihuwar Tijjani hakan yasa suka dauki son duniya suka dora masa sedai Allah beyi zasuyi doguwar rayuwa tare ba domin kuwa shekarun Tijjani bakwai a Duniya Mahaifinsa Malam Lawan Me gari ya rasu wata hudu tsakani ya rage kwanaki goma Goggo Asabe ta fita daga takabarsa itama ta amsa kiran Mahaliccinta shikenan Tijjani ya tashi maraya gaba da baya riqonsa ya koma tsakanin dangin Mahaifinsa yau yana wannan gida gobe yana na can wanda gaba dayansu sunayi ne saboda tarin dukiyar qasar da Mahaifinsa ya mutu ya bar masa ba kuma sun bari ya girma ya samu komai ba se wata gona kwalli daya wadda itama wani qanin mahaifiyarsa ne yayi tsayin daka gurin ganin bata salwantaba se fili wanda gidan da iyayensa suka zauna ya kamachi a bashi amma Sabon me garin da aka nada wanda yake qanin Mahaifinsa ya gaje ya shiga ya zauna a ciki dukda cewar gadon Tijjani ne, badan ma suna tsoron tijarar Kawun nasa ba shine dalilin daya saka ya bashi wani fili daban yace ya gina.

‎Da wannan gona daya tsira da ita yaci gaba da kula da rayuwarsa ita yake nomawa abinda ya samu ya siyar yayi buqatunsa har yayi aure ya auri Fadi yar Kawunsa yayan mahaifiyarsa haka suka zauna tsayin shekaru cikin rufin Asirin Allah har tayi yaya biyar Maza uku mata uku Lawan da suke kira Baba se Hashimu, Maryam, Amina, Aminu da kuma Zulai. Bayan Baba da Hashimu sun tasa su suka cigaba da taimaka masa da gonar da ita kadai ce hanyar samunsu, abinda suka noma a ciki zaau cire abinci, ragowar a siyar a ringa buqatun yau da kullum wannan dalili ya saka rani damina koda yaushe cikin shuka yake musamman da Allah ya taimakeshi gonar tasa tana kusa da wata fadama dan haka bashida matsalar ruwa sabodan noman rani sannan tana da girma babu laifi shiyasa yake noma nau'ikan abici kala kala.

‎Suna zaune lafiya da Fadi lokaci daya ya bijiro da zancen son qarin aure bayan daya hadu da Hafsatu Farar bafillatana baquwa da sukazo qauyensu kawo Amarya Tijjani na ganinta yace tayi masa, be samu matsala da Fadi ba, inda ma yar tangardar take be wuce damuwar yanda al'amura zasu kaya musu ba idan ya qaro auran dalili da cewar lallaba rayuwa sukeyi ba shida wata hanyar samun kudi idan ba noman nan da yakeyi ba dukda rayuwa nada sauqi a wancan lokacin amma nauyi ze qarar masa idan yayi auran, rarar da suke samu ta amfani gona har a siyar bw zama lallai aci gaba da samu ba tunda wacce ze auro din itama haihuqa zatayi wata rana wannan Fadi taso ta fahimtar dashi amma ya nuna komai na Allah ne shi yake ciyarwa kuma yanda ya nufeshi da qarin auran ze hore masa abinda ze cigaba da kulawa dasu haka kuwa akayi ya auro Hafsatu zaman au gwanin dadi da Fadi tana bata girma sosai a matsayinta na wadda ta girmeta kuma tana sama da ita a gidan aure wannan ladabi nata yake qarawa Malam Tijjani sonta.
‎Shekara daya ta haifi Da Namiji aka saka masa Yakubu, shekarar biyu ta haifi Audu se Bilkisu, Aisha da kuma Muktar me sunan Babanta suna ce masa Baballiya.

‎Rayuwa ta qarayiwa Malam Tijjani da iyalan sa tsanani saboda sun qara yawa kuma madogarar tasu dai guda daya ce wannan gona, qari da haka hatta da Maryo da Amina yayan Goggo Fadi da aka aurar mazajensu duk suma ba masu qarfi bane se ya zama har dasu ake noma gonar Malam Tijjanin abinda aka fitar a raba kowa yaje yayi ta jalautawa da iyalansa wannan matsatsin rayuwa ya saka Audu tashi da burin son yayi kudi saboda Baffansa ya huta da wahala. A lokacin farko shigowar Boko Yaro dayane a garin yake karatun Bokon Shamsu wanda yake dan Me gari shima ya kaishi cikin Kano ne yana zaune gidan wani Hakimi se shekara shekara yake zuwa gidan. Sa'an Yakubu ne amma duka Abokanai suke dasu Audu tunda tazarar shekarun ba yawa kuma tare suke karatun Allo kafin aka kaishi birni idan Shamsu yazo kuma zeyita bawa su Audu labarin Birni da Turawan da suke koya musu karatu har yace suyiwa Baffansu magana suma akai su dan Malamansu sun gaya musu idan suka dage sukayi karatu zasu samu aiki a ringa biyansu Albashi wadanda suka iya turanci kuma har Ingila zasu tafi dasu.

‎Zancen kudi da Audu yaji yasa hankalinsa ya tashi ya kuma quduri niyyar zuwa Birni Yakubu kuwa da tun qaraminsa ya tashi da Burin Zama Alqali, ko wasa akeyi zece shine Alqali ayita zuwa gabansa ana kawo shari'a shima Shamsu yace masa a birni da akwai Kotu ba irin yanda ake shari'a anan ba sedai aje gaban me gari. Audu yacewa Yakubu suyiwa Baffansu maganar zuwa Boko amma se yace Aa dan shi yana da sanyi ba kamar Audun ba yana gudun yiwa Baffan magana yayi masa fada dan lokacin da aka kai Shamsu be manta ba harda Baffansu a masu cewa an kaishi ze koyo yahudanci Audu beyi qasa a guiwa ba ya samu Mahaifiyarsu da suke cewa Dada da zancen tayiwa Baffa magana ya samu me gari idan Shamsu ze koma birni su bishi take kuwa ta nuna rashin amincrwa itama dai kamar Yakubu ta tuna masa da Mahaifinsa na Adawa da Karatun Boko da ya shigo daga nan aka bar maganar badan har zuciya Audu ya haqura ba sedai yayi shiru ne kawai zuwa wani lokaci saboda tunda yaji zancen kudi fa hankalinsa yayi kan Birni kuma kota halin qaqa dai se yaje shi.

‎Seda aka shekara kafin dama ta sake zuwar wa Audu a wannan Karon a gurin Malamin da yake musu karatun yaji cewar ze kai Yara Birni can tsangayar Malaminsa Gwani Musa a unguwar Kabara. Audu najin wannan batu yana komawa gida ya sanarwa da Dada a wannan karon itama bata ce Aa ba tasan kuma shima mahaifinsu baze hana ba inda zaa iya samun matsala be wuci yanzu da suka tasa ba suna taya sauran yan uwansu aikin Gona amma tasan hakan baze zama wani abu ba. Haka kuwa akayi ta damu Malam Tijjani da batun yayi na'am har yace ze samu Malam Tsalha malamin tsangayar tasu yaji kanun maganar, bayan duk shirye shiryen da suka kamata Audu da Yakubu suka bi tawagar Yaran Gari zuwa birni Almajiranci, dukda Malam Tijjani yaso iya Audu ya tafi Yakubu ya tsaya amma Audu ya kafe kaida fata se sun tafi tare saboda shirinsu na karatun Boko wanda Yakubu ya fishi buri akan abu shi neman kudi kawai yake so yaje yayi a Birni ba wani Karatun Allo kona boko ba.

‎Seda suka shafe wata uku a tsangayar Gwani Musa suna kuma karantar birnin na Kano, basu san inda zasu nemi Shamsu ba balle ya kaisu makarantarsu, Audu a shige shigensa yayi Abokanai anan cikin Magashi suka shaqu da wani Yaro Sa'an sa Hayatu yaron gidan da Audu yake yiwa aikace aikace ne. Hayatu da sauran yan uwansa suna makarantar boko dan haka Audu ya nuna masa shida dan uwansa Yakubu suna sha'awar karatu kuma abinda ya fito dasu daga qauye kenan. Hayatu ya sanarwa da Mahaifinsa wanda a lokacin suna cikin mutanen da suka karbi Boko sosai yaji dadi kwarai da wannan abu dan haka ba tareda bata lokaci ba yaje da kansa ya samu Gwani Musa ya sanar masa da buqatar su Audu tayin karatun Boko. Da yake Malami ne me fahimta kuma shi kansa cikin yayansa akwai wadanda suke Bokon saboda yanda Sarakuna da masu kudi da suke samun damar fita Waje suke fada musu Alfanun Bokon be hanasu Audu ba, ya kafa musu sharadi dai na dole zasu cigaba da daukar Karatu, da safe suje bokonsu su dawo Yamma da dare su zauna a makaranta suyi karatun Qur'ani haka kuwa akayi su Audu suka fara zuwa makaranta shekara daya da haka yace shi ya gaji saboda Shamsu ce masa yayi idan anyi karatu za'a samu aiki a samu kudi shi kuwa kullum karatu ake dora musu bema ji ranar da za'a gama ba dan shekaru ake lissafowa Yakubu ne yayi ta tausarsa akan yayi haquri da sannu zasu kai matakin da suke buri.

‎Haka suka ci gaba, Yakubu na matuqar maida hankali ga Karatu yayinda Audu turanci kawai ya saka zuciyarsa ze koya saboda idan ta tabbata sun gama makaranta za'a kaisu turai kar yaje ya rasa bakin magana. A hankali ya faratiwa Makarar asha ruwan tsuntsaye, Sadi, da aka kawosu Almajiranta tare amma shi dan Bagwai ne shiya fara nuna masa hanyar Kasuwa. Da safe idan sun tafi Boko shida Yakubu ze zame ya tafi bakin Asibiti anan zeyi duk wani aiki daya samu, dako ne, aike, duk wani abu da zeyi a biyashi haka ya ringayi kan jiki kan qarfi dake ya saka abin a ransa kuma yana da zuciyar yi se gashi baya jin wahalar kowanne irin aiki indai ze kawo masa kudi.

‎Da Yakubu ya gane baya zama a makaranta yace ze gayawa Malam seya dakata da zuwa Kasuwa, cikin yan kudaden daya samu ya auno Aya da gyada ya kaiwa Matar Malam da suke kira Nene dayake suna shiri yace tayi masa gyada me gishiri da Aya me siga ya daura abarsa a Boko ya siyar a Allo ya siyar se gashi an gane shi a unguwa Audu me gyada da Aya kuma sosai yake ciniki abinsa. Seda suka shekara biyu kafin sukaje gida, a lokacin sun fara zama samari dan Yakubu nada shekaru sha biyar Audu nada Sha uku. Cikin yan kudaden jarinsa yayiwa Dada da qannensa harda Baffansu tsaraba.

‎Kowa yaji dadin yanda ya gansu, Dada ce ta ringa masa fada akan ina ya samu kudi yayi wannan siyayya be boye mata ya sanar mata da duk abubuwan da yakeyi harda zancen Boko da sukeyi shida Yakubu ya kuma qara da fada mata gaskiyar dama saboda ya samu damar neman kudi Yakubu kuma yayi karatu yasa sukace zasu Makarantar Allon. A wannan karon kafin su koma seda ta sanar da mahaifinsu gaskiyar komai gudun kar wata rana ya gane yace sun hada baki sun munafurceta, da fari ya ringa fada dan sosai yake Adawa da karatun Boko har yana cewa ba zasu koma Birnin ba se kuma daga baya basu san yanda akayi ya canza ra'ayi ba da kansa yayi musu shirin komawa ya kuma yi musu nasiha tareda gargadin su tsaya a turbar Allah karsu yarda masu jajayen kunnuwa su dorasu akan wata hanya sabanin wadda Addinin Islama ya dora mu akai. Ya sake jawa Audu kunne sosai akan banbance tsakanin Halal da Haram tunda yana zuciyar nema baze daku she shi ba, abinda ya janyo masa sakkowa harya haqura zasu koma dinma bayan sunyi magana da Hashimu dansa na biyu shiya nuna masa Alfanun abinda su Audun sukeyi tunda baya kaucewa shari'a bane.

‎Yace masa "Baba idan ka dubi yanda rayuwa take tafiya a kullum abubuwa qara yi mana wahala sukeyi dan abinda muke nomawa ba wadatar mu yake yi ba balle har mu samu na siyarwa muyi sauran buqatu kuma ko a cikin karkarar nan idan ka duba masu fita fatauci Abokanan mu zakaga suna samun Abun rufin asiri har su taimaka mana muma, da ace tun muna qanana kamar su muma mun tashi da wannan tunanin qila da rayuwar ta mana sauqi amma yanzu tunda Allah yasa su sun himmatu zasuyi a barsu muyita rakasu da Addu'a Aminu ma da ze bisu suje can birnin yayi Bokon koya kama sana'a kamar Audu duk da hakan yayi".

‎To haka su Audu suka koma ba tareda Aminu ba dan yace ba zashi ba da yake Auta ne Goggo Fadi bata takura masa ba kuma shi kadai ya rage gabanta tunda duk an aurar da Maryo da Amina Mazan ma Hashimu da Lawan sunyi Aure. Rayuwa taci gaba da garawa Audu da Yakubu a birni, iya wuya Audu neman kudi yakeyi yana kuma riqe da hudubar Mahaifansa akan ya tsaya ga halal karya kuskura yaci abinda Allah be halasta masa ba kuma da yake a lokacin duniya na zaune lafiya cuta da bata gari basuyi yawa ba shiyasa abun yazo masa a sauqaqe. Tun yana Dako a kasuwa ko aikace aikace har ya fara kayi nayi, ze karbi kaya ya fita dasu ya siyar ya cire ribarsa har ta kai ya hada yar tireda yana kasa kayan koi gefe gida kuma ya ajiye Baro duk wani dan itace na marmari da ake yayi a lokaci ze saro ya ringa siyarwa yan kasuwar har mamakinsa suke ganinsa yaro qarami dukda yana da baragen girma amma zafin neman sa ba duk babbaba shiyasa yayi shura a bakin Asibiti babu wanda besan AUDU BECHI ba haka suke masa inkiya da garinsu.

‎Duk qarshen shekara suke zuwa gida kuma duk sanda zasu tafi haka ze hada tsaraba himili duk wanda ya shafe shi seya riqe masa wani abu ya kai masa dan badaga nan ba Audu akwai kyauta kuma a wannan yanayi Girma da Wahala suka fara kwantar da mahaifinsu dukda shekarunsa basu kai ace ya kwanta tun yanzu ba amma yanda rayuwar ta faro tun quruciya jiki yana wahalar data zarce abinda ze dauka shiya janyo masa ciwo yayi masa kwaf yau lafiya gobe babu haka yasa idan zasu je gida Audu ze siyi magungunan ya tafi masa dasu da irin mayukan zafi saboda qorafin ciwon jiki da yake yawanyi.

‎A wannan gantafalfala suka kammala Primary tareda Saukar alqur'ani ta biye wadda Audu dai ba zuwanta yake ba a sati befi ya leqa sau daya ba ita kanta Allon Karatun dare kadai yake zama Gwani yayi fadan yayi nasihar amma Audu ya toshe kunne, dadinta daya yana biya karatu daidai ya wanke Allonsa akan lokaci wannan yasa Gwani yake daga masa qafa Bokon ma idan ana jaraba zeje yayi kuma zeci ga turancin daya saka kansa ya iya radau dan ko Yakubu me qulafucin Bokon Albarka shiyasa Malaman suke ji dashi, Audu akwai rashin ji amma akwai kwakwalawar daukar Karatu.

‎Yakubu ya tafi makarantar kwana dan cigaba da karatun sa, burinsa ne ya zama Alqali Audu kuwa yace yayi sallama da Boko ya kama neman kudi kuma. Shi yayiwa Yakubu duk wani shiri na tafiya makarantar, haka kuma yana kai masa ziyara idan anyi hutu Yakubun Bechi yake tafiya yayi hutunsa acan Audu kuma ana Kano ana ta fafutukar rayuwa. Inda ya kafa yar tiredar tasa aikin fadada titi yabi ta gun dole ya tashi daga qarshe ya koma zuba kayan kolin nasa a Baro yayi ta zaga kasuwa yana waqa ta kiran customers yanda yake waqar abin dariya yake saka wasu siya badan ma sunyi niyya ba. Yakubu yana shekara ta uku a makaranta lokacin kuma aka aurar da Bilki wadda take bin Audu, ba qaramar Bajinta Audu yayi a auran nan ba dan dama ya dade yana tanadi saboda mutuniyarsa ce ko irin fadan

Karanta Next Chapter Matar Mutum