Auren Soja Part 3
...
kalli video din yakai sau uku yana repeat din shi dressing dinta yake karewa kallo har zuwa y'anda ta baje mai cikin kitchen ta hada mai miya a natse cikin kwarewa da kuma tsantsar tsabta,
Stop yasa dai dai lokacin da ta jijiga jikinta a gaban zuby zata zabga masifa d'an karamin bakinta ya tsurawa ido har zuwa lips din masu sheki da kuma idanun ta masu kama da fish lashes dinta sunyi zaro zaro ga gefen fuskar ta suma akwance tana sheki da Alamar taji gyara,
Samun kanshi yayi da jin nishadi karfe sha biyu ya bar office yace su tafi gida shima bai San dalilin shi na son komawar ba kasan cewar shi mutum mai son Aikin shi baya son wasa ko kadan,
Gefen mutane biyu kuwa sai zullumi sukeyi domin basu San me ogan nasu zaiyi ba yau wato EMA da Ahmed,
Motar su na tsaya wa sojojin shi suka bude mai motar ya fito kawai ya samu kanshi da wai gawa kofar gidan Ahmed din bakowa a wurin,
Saida gaban Ahmed ya fadi domin yasan wa yake kallo Yarinyar nan tajamun gidan ya shiga EMA tuni ya tsure tun jin jiniyar motar ta ogan don yasan lokacin dawowar shi baiyi ba
Tundaga kofar falon ya cire rigar saman ta kaki ya rataya a wani abin rataya kaya ya zauna a kan kujera tareda dora kafa daya kan daya yana girgiza wa,
Ahmed na shigomai da kayan shi ya nufi hanyar fita tsayar dashi yayi tareda bashi umarnin yayi serving dinshi Abinci,
Kallon shi yayi domin baiyi tunanin zaici Abincin da yana gani Yasmin ta hada shi ba, da sauri ya nufi kitchen ya samu EMA na sintiri hannu saman kai ya daka mai tsawa,
Ya natsu tareda bashi umarnin aje ya shirya table din oga, sanin halin EMA yanzu zai kuma tafka wani shirmen yasa ya hada mai komai da kanshi ya zuba ya jera a kan table din dake gefen shi ya zuba mai komai tareda dakko mai ruwa mai sanyi har da coke ya Ajiye a gefe sannan ya fita domin zuwa jawa uwar rigima kunne,
Tashi yayi ya zubawa plate din miyar idanu tayi gwanin sha'awa miyar batayi mugun yauki ba yasa mu kanshi da daukar spoon ya deba yakai bakin shi saida ya rintse idanun shi tsabar dad'in da ya ratsa shi,
Bai San lokacin da ya shanye miyar tas ba batareda ya ko kalli tuwon semon da EMA ya tuka mai ba ya dauki ruwa ya kora yaji ya koshi tab kamar yaci wani Abu,
Gaskiya girki hannu ne sirri ne kuma ga duk macen da tasan me takeyi ko ruwa ta dafa na tea zakaji shi daban
Ko takan EMA bai biba ya haye sama ya fada wanka EMA na ganin ya tashi ya fito ya tattara kayan yayi kitchen da gudu tareda Addu'ar kar ya shiga hannun oga,
*UMMU AMMAR*
[8/30, 2:56 PM] Feenerh Wrtr: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
_*BARIKI*_
_Auren soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
_written by fenerh_
Maman Ammar
*Dedicated to*
Fiddousi mainasara
5&6
......Ahmed na shiga gidan nashi ya sameta a baje ita da yaron ta a falon sai cin Abin cinta takeyi hankali kwance shi kuma ta jefa shi a zullumi,
Gaishe shi tayi ya zauna a kusa da ita tareda daukar yaron shi "ina Maryam take? " Aunty na hutawa bacci takeyi bari in kawo ma Abinci,
Ta fada tana shirin mikewa yace "no zo Muyi magana Yasmin, yakira sunan ta tasan kwanan zancen don haka ko a jikin ta ta koma ta zauna tareda zabga mai na mujiya,
Dariya ya yi ganin reaction dinta, " Yasmin haka kikeyi a school? "Kallon Bangane ba tayi mai, " eh naga kinada mugun karfin hali ne wanda ba haka Maryam take ba ita matata batason fitina bata son matsala Amma ke naga idan ma matsalar batazo ba da kanki kike tara kai ki kirata tazo,
"Yaya Ahmed Nafasan me kake son fada' ta fada tana turo baki " hhhh yayi dariya kafin ya cigaba,
"Nasan kinsan me kikayi ai, " Amma so kike a kulle ni ne kinsan laifin zai iya komawa Kaina?
"Oga nane kuma Yarinyar da kika yima wulakanci bakisan tsakanin su ba " oga Muhammad na matukar jida ita tanada muhim manci a rayuwar shi ita kadai ce macen da ya dade da ita kuma nake sa ran zai iya Auren ta duk da bansan zuciyar shi ba amma kowa yasan kusan cin su,
"To ni ya Ahmed ina ruwa na dasu ? " me kikaje yi gidan oga dazu? "Nifa taimako nayi Emanuel ne.... Ta yi mai bayanin y'anda sukayi dashi yayi shiru,
" amma Yasmin duk barikin nan kirasa wanda zakiyi mutumci dashi sai EMA? "Kaji yaya to sai inki mai sona? " aa ban fada ba nidai a kiyaye kar ajamin matsala da aiki na,
Tashi tayi kawai tare da duba sakon da yashigo wayar ta , wani murmushin mugun ta tayi kafin ta yi tsaki "zanci ubanki maman Amla sai nasa jinin ki ya hau,
Dama bayan Fitowar ta daga gidan MA tayi karo da Baban Amla sukayi musayar number yace zai kirata suyi hira da dare
Ganin sakon da ya turo mata yanzu yasa ta kara d'ana tarko,
_zan kiraki Anjima Muyi hira face to face domin kin tafi da zuciya ta har ma da murad'i na_
Reply ta tura mai
_saika zo ina nan ina jiran ka I love you_
Ta tura tana tun tsura dariya, ai kuwa jiki na rawa ya kirata kai tsaye a lokacin yana zaune da Matar shi ya mike ya fito don kawai yaji muryar ta,
Ba bata lokaci ta d'auka tare da karya murya " Aslm Alkm "Wslm gimbiya kin rikita ni gaba daya na matsu ban ganki ba pls ki leko ko sau daya inyi tozali da kyakkyawar fuskar ki ko zanji dad'i,
Wata irin dariya tayi mai tafiya da ruhi tace " Karka damu zaka ganni sai ma ka gaji da gani na' "Allah kar ya nufe ni da gajiya da ganin ki gimbiya,
" sai Anjima yanzu ina busy ne' "ok bye gimbiya ta, ta katse wayar tareda tunawa da bakar fuskar shi tace " god forbid bad thing,
Karfe takwas na daren ranar yasha wanka tareda nufo kofar gidan nasu ya kirata a waya,
Tana zaune suna hira da Aunty Maryam ta ce "ina zuwa Aunty nayi bako,
" zaro ido tayi waje "yaushe kika fara kula samari Yasmin? " kaji Aunty ban isa bane? "Am nineteen fa going to twenty,
Naji kije kidawo kifada min waye? " ok ta fada saida ta koma ciki ta kara gyara fuskar ta tareda fesa turare mai laushin kamshi sannan ta yafo gyale akan doguwar rigar jikin ta,
Tayi matukar yin kyau kamar ka sace ta ka gudu ta fito cikin taku dai dai, yana hango Fitowar ta ya kashe ta da ido kamar ya hadiye ta yakeji Babyn ta mugun tafiya da tunanin ruhin shi,
"Barka da fitowa gimbiyar Umar, murmushi tayi itama tareda cewa barka da dare'
Namiji muna fuki saida ya kalli kofar gidan shi sannan ya ce mu dan matsa can nan haske yayi yawa banason sa ido, batareda ta damu ba suka matsa d'an gaba kadan wanda tana hango harabar gidan na Oga kwata kwata kuma idan ba karya idanun ta ke mata ba tana hango mutum ta saman benen ta waje wurin da Akayi domin shan iska kuma idan mutum na wurin yana iya hango duk Abubuwan dake faruwa akusa ,
Sharewa tayi kawai suka fara zuba hira kasan cewar ta mai son zance tuni ta saki jiki da shi har tana dariya, hasken wayar shi ya haska fuskar ta,
" gimbiya ina fatan ba w'anda ya riga ni ko? "Aa ni banida saurayi banda lokacin kowa, ta fada " kai Amma ni mai sa'a ne Ashe,
Gyara tsayuwar shi yayi tareda d'an riko gefen gyalen ta "baby kin fa hadu sosai Allah yayi miki kira mai kyau komai yaji,
Shiyasa gaba daya kika tafi da ima nina, " Anzo wajen ta fada tareda kok'arin janye gyalen ta Amma da yake d'an duniya ne tuni ya rike hannun ta tamau,
Wani irin laushi yaji a hannun kamar na jariri ya lumshe idanu "wow gimbiya hannun ki keda wannan laushin Inaga.......
Fisge hannun ta tayi cikin fushi tareda matsawa kadan " bana son irin haka fa shiyasa naki kula samarin yanzun nan kai ma zamu bata idan ka kuma irin haka,
"Oh gimbiya sai kace rainon kyauye? Keda nake ganin ki a waye ''ba irin wannan waye war nayi ba don haka saida safe,
Ta juya cike da takaicin rike mata hannu da yayi d'an iska gobe zan cika aiki na in watsar da kai shege,
Kiran ta yake tayi amma ko juyowa batayi ba tayi shigewar ta gida,
Muhammad kuwa tun lokacin da ya haska fuskar ta yaga irin dariyar da takeyi yaji zuciyar shi tayi mai baki ya miki tareda dunkule hannun shi kamar zai daki mutum
Ganin ya riko hannun ta ai tuni ya wuce cikin gidan don ji yayi jinin shi na harbawa kamar zai tsiyaye a jinin shi,
Daga karshe wurin motsa jikin shi ya nufa yafara daga wani heavyweight da ko za a hada mu mu goma baza mu iya daga shi ba,
Saida ya hada gumi kamar w'anda ya fito filin daga ya mike tareda daukar ruwa mai sanyi ya sheka wa kanshi,
Towel ya d'auka ya fara tsane jikin shi dake tsiyaya kafin ya wurgar a zafafe ya jefar ya nufi bathroom ya sakarwa kanshi shower batareda ya cire gajeran wandon jikin shi ba,
Saida ya dauki lokaci mai tsawo a tsakiyar ruwan kafin ya fito daure da towel ya fada gado, bai taba tsintar zuciyar shi so restless ba irin yau meke damun shi ?
Ya rasa me yasa shi jin yanayin da yake ciki kodan sunyi fada ne da zuby? Runtse idon shi yayi gam tareda dunkule Hannayen shi yana maida numfashi mai zafi ji yake kanshi na juya wa,
Jin ankwanta a bayan shi yasa shi saurin zabura ya juyo domin ganin wace shegiyar ce ta isa da har ta shigo mai gida batareda ya kirata ba kuma for that matter har bedroom dinshi,
Ganin fuskar zuby yasa ya d'an yi cool dwan ya maida wukar fadan komawa jikin shi tayi tareda sa mai kuka ,
"Me yasa zaka hora ni haka Muhammad ? Kasan ina matukar kaunar ka me yasa zaka yimun haka ? Na tanbayi Ahmed yace mun kanwar shi ce ba Matar ka ba ce Am sorry baby for what I did,
" a jiyar zuciya ya sauke tareda cireta a jikin shi yace "is ok kinsan banason raini ai " riko hanun shi tayi masu burgeta saboda wasu jijiyoyi da suka shata ko ina kana gani kasan na karfi ne tareda motsa jiki,
Kallon shi takeyi wani iri Kamar hoto domin ba haka yake ba ya canja "meke damun ka Muhammad dina? " waya bata baka rai ? Nasan Muhammad din zubaida ba haka yake ba why the sudden change?
"Ni ba wani canji ke ke ganin haka, " ok ya isa ni dai hakuri nazo bayar wa don haka let me take a bath and come you no I really miss you ta fada tana daga gira,
Saurin tsayar da ita yayi "no need ki koma gida bana bukatar komai sai hutu yau please no aguement,
Sanin hali yasa taja ta tsaya tareda zuba mai ido kafin ta dauki key din motar ta ta fita kawai kafin ya kuma hawa,
Runtse idanun shi yayi gam yarasa meke damun shi ji yake kamar ya mike ya dawo da zuby amma ina yasan zataso ya taba ta shi kuma yagaji da wahalar da jikin shi batareda ya samu Abin da yakeso ba,
" wai haka ne matan suke? To meye zaisa yayi Aure tunda shidai har yau baiji wani Abin da zaisa yace zaiyi Aure ba, sex food what ?
Shidai yasan ko mace goma yakeso a rana zai samu but meye dadi a cikin su duk Abin daya ne shi har yau bai samu ruwan da zai kashe mai kishi ba har yau gobarar cikin shi na ci
Shi mace ma duk wadda ya taba bayajin wani feelings he is just using them to reduced the fluid
__________
Umar ya kirata yafi sau goma taki dagawa Shikuwa a halin yanzu baijin zai iya hakura da ita har dai da yaji irin taushin dake jikin ta yasha cudanya da mata Amma ita da ban ce shi gaba daya ma ya canja akalar zuciyar daga samun biyan bukata zuwa mallakar ta gaba daya Auren ta zaiyi kawai,
A ranar Sam Matar shi bata gane mai ba domin ya mugun daure mata fuska karshe ma ko makwanci yaki hada wa da ita,
Falo ya dawo sai faman text yake turawa Yasmin na lallashi Amma ina tama yi nisa ita a bacci tareda ku durin cin uban maman Amla da safe,
Tana tashi da sakon nin shi tayi karo dariyar mugunta tayi mai kafin ta tura mai msg
_Zamu hadu kafin kaje aiki by_
Ta fara taya y'ar uwar ta aiki tana cike da nishadi w'anda saida Maryam tayi magana "Yasmin me ke faruwa? Nifa ban gane miki ba Sam '
" bakomai Aunty na kawai naji dad'in wannan ziyarar da na kawo muku ne jina nake cikin farin ciki tun zuwa na, Hmm kawai Maryam tace kafin tace....
"Allah yasa ba wani Abun kike hadawa ba , Ameen ta Amsa saida suka kammala Aikin gidan ta fada wanka shirya wa tayi cikin wata riga da wandon Pakistan purple wandon fari tayi matukar yin kyau ta gyara gashin ta mai tsawo tareda dunkule shi gyale fari d'an karami ta yafa ta fesa turare ta fito,
Wani sheki takeyi ga kayan sunyi matukar karbar ta rigar ta d'an kamata ta West ga wandon pencil silipas ts sanya masu d'an tudu ta dauki wayar ta ta kirashi,
A lokacin zaune yake Matar shi sai zuba take amma hankalin shi na kan wayar shi duk da yayi late Amma Bazai taba tafiya bai ganta ba,,
Motoci tagani a kofar katon gate din a Jere hilux biyu da kuma wata Benz Army colour a tsakiya sojoji ne a tsaye da bindi gogi kamar zasu ci babu dauke kanta tayi duk da taji tsoro saida ta kusa kofar gidan na Umar ta kirashi " ka fito ina waje,
Wani irib zabura yayi kamar wani maye ya fito batareda yako kalli Matar shi ba jikin shi na rawa , meke damun Baban Amla ne wai ta fada tareda biyo bayan shi,
Lokacin har ya karaso kusa da ita kamar zai rungumo ta "gimbiya kin sani cikin wani hali wallahi na horu da yawa a Gaskiya kin gama tafiya da zuciyar Umar,
Murmushi tayi na mugunta domin hankalin ta na kofar gidan nashi kuma ta hango Matar shi tsaye ta dora hannu akai hawaye na zuba,
Karaso wa tayi kamar guguwa ta matso " Amma Allah ya isa tsakani na dake wallahi karuwa kawai masu shigowa bariki domin kwace mazan mutane a haka zaku kare tsinan nu,
Wani irin tsawa ya buga mata tareda yi mata tsatstsauran gargadi "hauwa ki wuce kafin yanzu in canja Shawara akan ki wallahi,
Tasan halin shi dole ta wuce cikin gidan tana kuka kafin ya nad'a mata na jaki tana wucewa Yasmin ta juya zata tafi domin burin ta ya cika tasan yanzu can ta matse musu ko ya lallashi Matar shi ko yayi biyu babu,
Shan gaban ta yayi jikin shi na rawa " Yasmin please kiyi hakuri zan ja mata kunne k'arki tafi ki barni cikin damuwa,
Tsayawa tayi cikin daure fuska "aini ban ma San kanada Aure ba da ban saurare ka tun farko ba kuma indai wannan ce Matar ka wallahi ban Auren ka don ba tun yau ts saba Zagina ba don haka ka kama kanka dani kafin in hada ka da yaya na,
" what is happening? Taji muryar Ahmed saurin juyawa tayi wurin shi "Yauwa ya Ahmed ka shiga tsakani na da wannan mutumin yasa min ido ka man iyaka dashi ko dole ne in soshi tayi shigewar ta cikin gidan batareda ta ko saurari Ahmed din ba,,
Muhammad da ya fito daga gidan shi har ya shiga cikin motar shi yaga duk Abin da ya faru yana hango su daga cikin motar har Fitowar Ahmed da wucewar ta ciki,
This girl is unbelievable meke damun ta ta hada shi da budurwar shi yanzu kuma miji da mata bayan sun gama shan soyayyar su,
Isowar Ahmed cikin motar yasa shi dawowa cikin dogon tunanin da yakeyi gaida shi yayi cikin respect irin nasu na sojoji sannan aka rufe motar suka kama hanya,
Sai bayan sun isa office ya kirashi office, " Ahmed meke faruwa ne dazu I saw everything me ka fadawa Umar? Me yake tsakanin su da sister ka?
"Oga wai yana sonta ne kuma yanzu tace ya fita hanyar ta ni ban gane me ke faruwa ba shima nace ya jirani har mu dawo gida Muyi magana domin nasan halin Yasmin,
" Yasmin'''' ya furta sunan can kasan zuciyar shi sunan ta Akwai dad'i sosai,
Ka fada mai karya kuma gangan cin zuwa gidanka tunda tace ya kyale ta ba a so dole don haka warn him before I do something about it
"Ok sir I will do so , ya sallame shi tareda maida bayan shi bayan kujera ya runtse idanun shi yana wani irin murmushi " what a woman Yarinyar nan me take nufi da rayuwar suda ta shigo bariki ?
*I don't no kuci gaba da biyo ni,"*
*UMMU AMMAR*
[8/30, 2:56 PM] Feenerh Wrtr: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
_*BARIKI*_
_Auren soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
_written by fenerh_
Maman Ammar
*Dedicated to*
Fiddousi mainasara
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
7&8
Maryam batasan wainar da ake toyawa ba saida Maman Amla ta zo gidan da kanta tana uban kuka,
Har kasa tasa guiwoyin ta tana rokon Maryam don Allah su bar mata mijin ta gaba daya yace idan bai samu Yasmin ba itama zata barmai gida,
Abin ya bama Aunty Maryam mamaki ganin ko a jikin