Auren Soja Part 2



‎ya kara labto musu wata bakar maganar, Shigowar Ahmed ne yasa momy tasaki fara'a "Amadu dama tare kuke?


‎" eh mama ina wuni? "Lafiya lau d'an Albarka ya iyali, ? Ina labarin y'ar Albarka Yasmin? " ai momy dazu kuwa tazo bariki tazo mana hutu,


‎"Ai yar nan nada hankali sai daya kawai da kukazo tayi mugun shiga zuciya ta, kallon Momyn nashi yayi kafin ya kalli Ahmed yace " who is Yasmin?


‎"Oga that my sister, tabe baki yayi kafin yace yaushe kukazo nan har momy ta ganta? Last time datazo ka aikoni lokacin zata tafi muka biyo nan kafin in sauke ta gida,


‎Shiru kawai yayi domin yasan halin Momyn shi idan taso mutum, " Muhammadu yaushe zanga Auren ka ? Idan Bakada zabine ni inmaka zabi kuma nasan zakayi farin ciki,

‎.

‎"Momy Muyi magana mai ma ana don Allah Mubar wannan, " oh wannan batada ma'sna kenan ? "Muhammadu idan lafiya ce Bakada ka fada min anemi magani shekarar ka talatin da bakwai yanzu kakusa arbain kullum ba wai yarinta kake karawa ba shekarun ka natafiya ne fa, Amadu ka fadawa Abokin ka ko mai gidanka zance ne oho domin nasan baida wani Abokin da zai iya fadawa matsalar shi sama dakai,


‎"In Akwai matsala kufada min, ta fada cike da damuwa aranta, saurin riko hannun ta yayi tareda rage murya a hankali,


‎" momy na kiyimin hakuri zanyi kok'arin yin hakan idan na shirya banason inyi Auren da zan shiga damuwa insa Kaina a matsala momy kitayani Addu'a kawai,



‎Tashi yayi tareda kallon Ahmed da idanun shi da sukayi ja saboda tausayin mahaifiyar tashi "muje ko dafatan bakwa bukatar komai?


‎Ya tanbaye ta Amma ido kawai ta zuba mai domin babbar bukatar ta itace Auren tilon d'an nata ta kuma ga jinin shi a duniya,



‎Yana fadawa motar ya jefar da wayar shi ya dafe goshin shi da yafara Sara mai Ahmed ya tayar da ita sai da suka tsaya bakin unguwar shanu sannan yace " oga Gasu nan fa sai ka zaba,


‎Daga jajayen idanun shi yayi ya zuba wurin matan dake Jere akan titi da shiga kamar Tsirara




‎Fita Ahmed yayi saida yayi ma wata magana tareda Ciro bandir din kudi ya bata ya dawo cikin motar "oga na yi making Arrangement din,



‎" ok muje mess ", ya fada kai tsaye suka wuce batareda sun tafi da ita ba,




‎Karfe kusan tara nadare suka dawo, kasan cewar lokacin zafine kusan mafi. Yawancin mutane kan fito waje domin shan iska duk da kuwa Akwai wutar lantarki ta ko ina ga A.c


‎Amma sanin kowane iskar ubangiji tafi kowace iskar bature ni ima tareda Amfani a jikin dan Adam,



‎Hirar su sukeyi irin ta y'an Uwa gefe data bowl ne dauke da chips Yasmin ta Ajiye agefen ta wandone ajikinta dogo mai fadi sosai da wata tea shirt mai guntun hannu ta kamata tsam kanta sanye da hular net kafar ta kuwa silipas ne sabo tayi matukar yin kyau sosai duk da bawai kwalliya tayi ba,


‎Amma she look very Adorable kamar ka sace ta ka gudu Babyn ta hadu sosai kamar y'ar Aljana ga kirjin nan cike tab da dukiyar Fulani daga kasa kuwa zakasan Allah yayi halitta a wurin nan mai daukar hankali,



‎Maryam ta kalle ta " Yasmin kije ki saka hijabi kinga yadda mijin maman Amla ya kasa shiga cikin gida tun dazu saboda ganin ki a nan kuma ga shigar dake jikin ki,



‎"Kyale tsinan ne Matar shi naciki tana jiran shi Amma ya tsaya kallo na Ayya kuwa sai na haukata shi,


‎" nidai ki rufamin Asiri kina ganin Matar nida ita saidai gaisuwa daga nesa saboda tsabar kishi tun zuwan ki na farko tazo nan tayi min magana "wai me yasa mukeson kawo kannin mu mata bariki neman maza?



‎" Kwal uba kika ce mata mene? "Hakuri na bata nace nidai ba neman miji kika zoyi ba zumunci ya kawoki tayi hakuri,



‎" ai wallahi sai nayi maganin ta Allah ya kai mu gobe bari ma kigani tun yanzu in dana tarko,


‎Mikewa tayi cikin salon daukar hankali har tana girgiza kirjin ta wanda suka yi d'an rawa kadan da saida numfashin shi yayi skipped sannan ta duk'a ta dauki bowl din chips din da takeci,



‎Ta kalli y'ar uwar ta "muje ciki Aunty ai munsha iska sosai ga boy na yayi bacci, baza mai duwai wukan ta tayi da gangan saida ta saka kafar ta cikin falon ta juyo tareda jefa mai blow kiss har da kashe mai ido daya cike da salon daukar magana



‎Ta fada cikin falon, kusan sumewa yayi a tsaye yakai hannun shi saitin wandon shi ya dafe saida ya dauki lokaci kafin ya daure fuska tamau ya shige cikin gidan nashi shima dauke da kudurin samun wannan Aljanar Yarinyar daga gani yar hannu ce,



‎Ita kuwa tana shiga ta kyal kyale da dariyar mugunta " ai zaki ga BARIKI maman Amla,


‎"Dariyar me kikeyi Yasmin? Ina fatan ba wani mugun Abin zaki kulla ba domin nasan halinki sarai dariyar ki ba Alkhairi bace,


‎" kai Aunty na ba komai kawai inajin nishad'i ne' "Hmmm Allah yasa, ta wuce masaukin ta wato dakin y'ar uwarta domin bin lafiyar gado saidai kwanciyar ta keda wuya ba Abinda ya fado mata sai fuskar wannan gayen,



‎" me yasa kake neman mata? Shine kawai ta samu bakin ta da furtawa tarasa dalilin da yasa taji kawai tsanar shi ta ragu a cikin ranta tunda ta ga fuskar shi a karon farko,



‎Kirar jikin shi domin ta hango irin muscles din da ya Ajiye na karfi w'anda tasan ba shakka idan ya riki namiji zai ji jiki bare mace,

‎His face look innocent he look pure but why is he like that? Saurin runtse idanun ta tayi tareda yin Addu'a har barawon ya dauke ta,



‎*"farkon farawa kenan my fans ina fatan wannan labari nawa da na faro ya baku ni shadin da kuke bukatar samu ya kuma ilmantar daku ya fadakar*



‎*"ku ci gaba da biyoni nidin ce dai "UMMU AMMAR Aunty Fener ku kuma Matar soja*
‎🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
‎_*BARIKI*_
‎_Auren soja_
‎🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻


‎_written by fenerh_
‎Maman Ammar



‎*Dedicated to*
‎Fiddousi mainasara

‎3&4

‎Kasan cewar ta saba tashi da wuri, yasa ko a gidan y'ar uwar tata ta tashi tun karfe shida tafara gyara musu gidan,


‎Ita ta shirya breakfast na gargajiya koko da kosai domin basa rabo da ni kak'ken wake a firij domin k'arin safe,



‎Saida ta kammala da wannan ta kwashi kayan su ta fita domin d'aurayewa, tana fitowa taci karo da maman Amla na tsaye tana kallon gidan nasu,



‎Daga murya tayi tareda cewa "ina kwana maman Amla mun sameku lafiya? Wata irin muguwar harara ta zabga mata tareda maka mata mugun tsaki ta shige tareda cewa " karuwan banza masu kwace mazan mutane kawai,



‎Dariya Yasmin tayi ta girgiza kai "zakiga karuwa ganin idon ki karamar y'ar bariki sai na koya miki darasi,





‎Tafada can kasan zuciyar ta domin batason tayi wata hayaniya da Matar Aure Ace tayi rashin kunya Amma sai ta gasa ta a ruwan sanyi zata koya mata hankali,


‎Wankin ta tayi ta shanya kasan cewar ba yawa ta koma ciki lokacin har Ahmed ya shirya cikin kakin shi ya fito fes Maryam na rike da hannun shi tana cewa,


‎....yanzu dear Bazaka sha ko tea ba? " Nop nayi latti kuma kinga mun makara yau, Shigowar ta yasa suka kalleta ganin ta rike da bocket "Yasmin har kintashi?


‎" ina kwanan ku ta fada tareda kallon mijin yayar ta "ni ai tun karfe shida Natashi da yake ku yan gayu ne kalli karfe takwas fa yanzu,



‎" eh bakyason matata ta huta ne ? "Inaso y'ar uwata ta huta don haka nayi mata Aikin komai har breakfast nayi muku yau,


‎" wow kanwata godiya nake bari ingani yafada yana matsawa wurin d'an karamin table dinsu ya bude flask yaga koko da kosai,


‎"Gaskiya kin burgeni kanwata a zuba min idan naje office zansha Acan nayi latti oga na jira na yanzu,.


‎Juyawa kawai tayi ta nemi flask me kyau ta zuba mai koko da kosan yayar ta karba ta rakashi har waje kafin ta dawo cikin gidan,



‎Kukan yaron Yane yasa ta nufi cikin dakin ta dakko shi dakan ta tayi mai wanka ta shirya shi kafin yasha nonon shi,





‎Shirya wa tayi cikin kwalliyar ta mai matukar kyau da daukar hankalin duk wani namiji, riga da wandone tasaka sunfito da surar ta mai kyau duk da rigar takai har guiwar ta,



‎Ta yafa d'an karamin mayafi ta fito tana zuba kamshi da kuma kyalli,
‎Taku take kamar wata Sarauniyar kyau tsabar jin kanta datakeyi,



‎Y'ar uwar ta ma saida tace " yayi Autar Mama wannan irin kyau haka saikace suruki na zai zo? Murmushi tayi kafin tace "kin manta kinada suruki a kusa Baban Amla,



‎" aa Yasmin kirufa min Asiri k'arki tafi kibarni da rigimar Matar nan don y'ar bala'i ce ta karshe wallahi, "takai karshen ta kuwa Aunty watch and see,



‎...nidai aa ki fita hanyar ta kawai, " hmm kawai tace tayi waje' "ina zakije? " shan iska zanfita "ki rufa min Asiri ki sanya hijabi Yasmin kinsan halin sojoji kuwa?


‎" wanda duk ya sa rai yasha wuya domin gani nan bari nan wallahi bani ba soja, shiru kawai tayi ta bita da kallo har ta fice,







‎Tana fitowa Emanuel na fitowa daga cikin gidan ya washe baki tareda nufota jikin shi na rawa"my friend '


‎"Yes wo good morning EMA, ya zauna gab da ita tareda zuba mata idanu domin tayi mugun yimai kyau, " chiii friend this kind fine no be small ting wo if my oga saw you Ahh,,,


‎Ya fada yana cizon yatsa basar da shirmen shi tayi tareda kawo wata hirar "why are you not going to office? " na because I dey cook for oga so I no dey go office,



‎"Friend oga bring one Celine Dione yerstaday no shape no boobs noting I don no wetin he go enjoy there wo?



‎Wani irin kallo ta watsa mai domin ya fara bata haushi da mu gayen hirar shin nan da baya gajiya kowa ya tanbaye shi oho?


‎Ta manta ita ke tanbayar shi a da can saboda gulma, kuma ita yau bata bukata impact zaman jiran Baban Amla takeyi Alakar sa idon can ta juya bata ta oga MA yanzu,



‎Ganin taki bashi fuska ya canja magana " I beg friend help me na oga say ma I cook kuka soup for him before he come back,



‎Kallon shi kawai tayi domin ya ishe ta da magana gashi da mugun nacin tsiya bata taba dana sanin sake mai fuska ba irin yau,



‎Cewa tayi ya tafi kawai zatazo ta nuna mai da fatan ogan shi Bazai dawo ya sameta ba yayi saurin girgiza kai "no oga no go comeback now till one O'Clock,



‎Saida ta fadawa Aunty Maryam ta fito suka wuce tare yana ta faman zabga mata magana,



‎Tundaga harabar gidan ta fara baza idanu fulawoyin da aka zagaye gidan sunyi matukar burgeta bata taba sanin haka wurin yakeba don bata taba matsawa ko jikin gate din dake zagaye da Bob ware ba ginin na tsakiyar shi,


‎Wani irin ni ima ke kadawa da ita ga kamshin furanni kala kala ga kayan mar mari zagaye da gidan irin su lemo gwanda mangwaro ayba har ma dasu gwaba,




‎Tsarin wurin ya matukar burgeta " hmm gidan mutum daya d'an iska yafi kuma kowa tsula iskan ci ogan y'an iska, ta fada aranta,



‎Falon gidan kuwa ai sai shuru kawai domin tsarin gidan gaba daya kamar Akwai mace saboda kyale kyale ga shi kalar komai favourite dinta purple and white,



‎Daga gefen kitchen din step da zai kaika upstairs din ne she wish zata iya hawa saman shima taga tsiyar dake ciki,




‎Maganar EMA ta dawo da ita ta bishi cikin kitchen din da ta kira Aljanar mace domin tana mugun son ganin kitchen a tsare ga wannan ya tsaru kamar a turai komai na bukatar macen data San kan kitchen Akwai a ciki,




‎Ajiyar zuciya ta sauke tareda ku durin idan zatayi Aure haka zata tsara nata insha Allah,



‎Da taimakon EMA ta hada komai ta shirya musu lafiyayyar miyar kuka da taji namomi zuku zuku aciki sai kamshin garlic da citta ke tashi domin sunada komai na Amfanin gargajiya da Alama ogan nason harkar gargajiya,




‎Shi kuwa EMA baki har kunne sai zuba yake mata kamar kanya har ta matsu tabar gidan tana kammalawa tace zata wuce ya rakota sai godiya yakeyi kamar ya ari baki,


‎"Tank you friend you save me today from my oga suna bude kofar shigowa wata sisi ta shigo kyakkyawa ce ba laifi ga wanka iya wanka domin less din jikin ta kadai zai nuna ma kudi sun koka Anan,



‎Komai na jikin ta kudi ne har Bangle's da jakar hanun ta Abin kallo ne sai walwali take tana zabga kamshi,



‎Wani irin kallo suke watsawa juna domin kowa na hango kyan kowa ita Yasmin Yarinyar burgeta tayi domin tana son mace mai daukar wanka kuma wannan tayi ba karya,




‎Ita kuwa zuby wani irin hade fuska tayi tana mata wani irin kallon ke wacece kafin ta bude baki cikin masifa tace,



‎" Emanuel who the hell is this? Tuni jikin shi ya fara rawa "sory madam na my friend I call her ne to help.......




‎" quiet ke kuma kiji nan nan gidan mijin da zan Aura ne ban y'arda ko wacce mace ta shigomin cikin shiba ni na tsara gidana kuma banason mace na rabar shi



‎Kinzo da kazaman kafar ki har cikin gidana to kar in kuma ganin ki daga yau stay away from my husband house,



‎Me neman kuka ai jikin Yasmin har rawa yakeyi ta gyara tsayuwar ta dakyau harda jijiga jikin da saida zuby tayi Addu'ar Allah yasa Muhammad bai taba ganin wannan Yarinyar ba,



‎"Ke wacece da zaki zo har cikin falo na kina min ihun wai gidan mijin ki lallai karuwan cin ki ya girma



‎" kin shigo min gidan Aure har kinada gut da zakice wai gidan mijin ki to ni Matar shi ce sai ki jira ya Auro ki kafin Kizo kiyimin gadara kuma yanzu kibar min gida kafin inhada ki da kuratan sojojin dake wajen gate din nan,




‎Wani irin tsuma jikin zuby ya farayi tuni hawaye suka wanke mata fuska wani irin kishi ne ya tokare mata kirji,



‎Kafin ta iya bude baki tayi magana kawai Yasmin ta turata waje ta datse kofar har tana huci kamar da gaske gidan tane,



‎EMA suman tsaye yayi ya dora hannu akai ya zama kamar statue duk da ba hausa yakeji ba yasan what ever Yasmin is saying is not right at All



‎"Chineke me friend na oga love wo na him girl friend she come from abroad you don kill me......



‎Tuni yafara paret tsaki ta yi tareda bude kofar ta leka taga ta tafi ta fito tayi wucewar ta gidan y'ar uwar ta ko ajikin ta,





‎A zaune yake a cikin office dinshi sanye da kakin shi yayi wani irin kyau a ciki gefen shi pistol ce da kuma system din shi har ma dasu tabs din shi akan table din ya dora kafafun shi dake sanye da boot dinshi masu sheki akai,




‎Kanshi a sama yana tunanin maganar shi da Momyn shi jiya, ta shigo cikin office din kamar yaki ta buga kofar jikin ta na rawa,


‎Har saida yayi saurin mikewa cikin hanzari ya janyo pistol dake gefen shi, ganin fuskar ta yasa yaji ranshi ya mugun baci,

‎.
‎Komawa yayi ya zauna kawai batareda yace mata ci kanki ba ta fara magana, " ka kyauta Muhammad na kiraka yakai sau uku jiya kaki daga min waya,


‎Bayan na fada maka zan dawo a jiya baka damu ba sannan d'an wulakanci na iso ko ka neme ni......any way nagano matsalar wato Aure kayi Muhammad bayan tafiya ta bayan kayi min Alkawarin Aure yanzu duk halaccin da nayi ma irin sakayyar da zaka biyani da ita kenan?




‎"All......." Quite don't you there couse me ke kika Ajiye ni ? Auren ki nayi ni nace ki jirani ? Na fada miki sai ke zan Aura ? How thare you banged into my office like this?




‎"Duk Rung's din da kikeyi a can na sani kar ki rena min hankali kuma Aure da kike magana....
‎Shiru yayi tareda kare matse fuska " eh nayi Aure kiyi Abinda zakiyi kuma yanzu kifitar min a office kafin inyi loosing control inci ubanki a nan '




‎Wani irin kuka ta fashe dashi kamar zata hadiye zuciya ta juya zata fita tana rufe baki yace "wait, tsaya wa tayi cak domin tayi tunanin hakuri zai bata,




‎" stay away from my wife and my house, da gudu tafice bako waiwaye duk inda ta wuce yaran shi kallon ta sukeyi domin kowa ya Santa dashi kuma sun San irin y'anda oga,ke mugun ji da ita to yau me ya faru,




‎Tana ficewa ya zauna kan kujera yana fitar da huci kamar kumurcin maciji yana tunani ko wace shegiya ce ta shigo mai gida har zuby ta ganta,?



‎Zaici uban Emanuel yau sai ya kulle shi don uban shi, baiso ya ma zuby haka ba Amma ai tasan bayason mace tayi mai gadara da rashin da'a shi yasa ya mata haka amma zai lallashe ta letter,



‎Intercoms ya danna Ahmed ya shigo saramai yayi ya koma gefe yana jiran umarni "ka hada min connection din TV inason inga wace ce a gidana?



‎" ok sir domin Akwai connection da yake ganin komai dake faruwa a gidan nashi Abinka da zamani,



‎Janyo tan din dake gaban shi yayi danna kawai yafara viewing Abinda ya faru na yau
‎Ahmed zare idanu yayi waje lokacin da video ya fara aiki,



‎Goshin shi ya dafe cike da kaduwa "wannan Yarinyar zata kashe ni waya aiketa gidan oga,?



‎MA kuwa tagumi yayi yana karewa karfin halin ta kallo mamakin ta ya mugun cika shi,


‎" og a....... Ahmed ya fada bakin shi na rawa zai bashi hakuri yayi saurin daga mai hannu tareda da nuna mai kofa yace ya fita kawai,




‎Jikin shi yayi sanyi ya fita shi kuwa ya


Karanta Next Chapter Auren Soja